Bayan faduwar rana, kauyuka da yawa dake nahiyar Afirka kan zauna tsit! Saboda duhu ya mamaye ko ina, kuma babu damar ci gaba da gudanar da wasu ayyuka. Sai dai a kauyen Koniobla dake dab da birnin Bamako na kasar Mali, ana iya ganin wani yanayi na daban, inda fitilu masu amfani da makamashin hasken rana ke haskaka tituna, kana akan ji karar shirye-shiryen telabijin daga gidajen mazauna kauyen.
A shekarar 2023, kasar Sin ta gudanar da wani aikin tallafi a kauyen Koniobla, da wuraren dake dab da shi, inda aka kafa na’urorin samar da wutar lantarki ta makamashin hasken rana 1195, da fitilun titi masu amfani da hasken rana 200, da fambo mai amfani da hasken rana guda 17, wadanda suka amfanar da mutane fiye da dubu 10. Hakan wani misali ne na yunkurin daidaita matsalar karancin wutar lantarki a Afirka ta hanyar hadin gwiwa tsakanin kasashe.
- CBN Ya Soke Cire Kuɗi Kyauta A ATM, Ya Ƙaddamar Da Sabbin Kuɗaɗen Caji
- Jarin Kadarori Da Sin Ta Zuba A Bangaren Layin Dogo Ya Kai Yuan Biliyan 43.9 A Janairu
Wani babban aiki dake gaban nahiyar Afirka shi ne samar da karin wutar lantarki, ganin yadda mutane kimanin miliyan 600 na nahiyar ke rassa samun damar amfani da wutar lantarki. A wajen taron koli kan batun makamashi na nahiyar Afirka da ya gudana a kasar Tanzaniya a kwanan baya, manyan kusoshi mahalarta taron sun jaddada bukatar dake akwai ta daidaita wannan matsala cikin sauri, kana an gabatar da shirin samar da wutar lantarki ta hanya mai dorewa ga karin mutane miliyan 300, ya zuwa shekarar 2030. Don neman cimma wannan buri ana bukatar zuba makudan kudi, da hadin kai da bangarori daban daban, kana kasar Sin ita ma za ta iya taka rawa a matsayin wata abokiyar hulda mai muhimmanci.
Sai dai watakila za ka so ka yi tambaya cewa, me ya sa za a zabi kasar Sin a matsayin abokiyar hulda a kokarin hadin gwiwa don samar da wutar lantarki mai tsabta a nahiyar Afirka?
To, dalili na farko shi ne, saboda tsakanin Afirka da Sin, akwai wata daddadiyar hulda ta hadin gwiwa mai kyau.
Labarai Masu Nasaba
Gaskiya Ta Bayyana Bayan Da Gwamnatin Amurka Ta Sanar Da Rufe USAID
DeepSeek: Kawar Da Shinge Ta Hanyar Kirkiro Sabbin Fasahohi
An ce, tsakanin shekarar 2000 zuwa 2023, kasar Sin ta samar da rance da yawansa ya kai kimanin dalar Amurka biliyan 43 ga kasashen Afirka, don su raya bangaren samar da wutar lantarki. Kana a shekarun nan, kamfanonin kasar Sin sun gudanar da dimbin ayyukan samar da wutar lantarki a nahiyar Afirka, kamarsu madatsar ruwa ta Souapiti ta kasar Guinea, da madatsar ruwa ta Djibloho dake kasar Guinea Bissau, da dai sauransu. Gaba daya an gudanar da ayyukan a kasashe da yankuna fiye da 40 na nahiyar, wadanda suka kara samar da wutar lantarki na kilowatt miliyan 120, da karin layin wutar lantarki mai tsawon kilomita dubu 66. Har ila yau, kasar Sin ta sanar da shirin gina wasu manyan ayyukan samar da wutar lantarki ta hanya mai tsbta guda 30 a nahiyar Afirka, cikin shekaru 3 masu zuwa, a taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka da ya gudana a bara.
Na biyu shi ne, fasahohin Sin a fannin zamanantarwar bangaren samar da wutar latarki suna da amfani ga kasashen Afirka a kokarinsu na raya kasa.
Kasar Sin ta kafa tsarin samar da wutar lantarki mai tsabta mafi girma a duniya, inda fitattun fasahohi da ta samu suka zamo masu rahusa kuma suka dace da yanayin da kasashen Afirka ke ciki. Kana kamfanonin kasar da suke taka muhimmiyar rawa a duniya a fannin sauya salon samar da makamashi mai tsabta, su ma za su iya taimaka wa kasashen Afirka kafa masana’antun hada injunan samar da wutar lantarki.
Na uku shi ne, Sin da Afirka sun cimma matsaya daya a fannin zamanantar da kasa ta hanya mai tsabta. A wajen taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka da ya gudana a bara, Sin da Afirka sun daddale yarjeniyoyi a bangarorin kara yin amfani da makamashi da ake sabuntawa a Afirka, da karfafa hadin gwiwar bangarorin samar da sabbin makamashi, da kara kaimi ga zamanantarwar tsarin kula da aikin makamashi na Afirka, da dai sauransu, wadanda suka nuna ra’ayi daya da kasashen Afirka da Sin suka samu a fannin manufar raya kasa. Hakan ya zo daidai da maganar da Cliff Mboya, masani dake aiki a cibiyar nazarin huldar Afirka da Sin ta kasar Ghana, ya fada, wato “Kasar Sin na kokarin daidaita manufofinta don neman dacewa da Ajandar shekarar 2063 da kungiyar kasashen Afirka AU ta gabatar”. (Bello Wang)